Labarai

‘Da na Kirista ne ba Musulmi ba – Mahaifin matashin Kirista da yayi yunkurin dasa ‘bam’

Sameul Ezekiel, mahaifin Nathaniel Samuel, matashin da aka kama yayin yunkurin dasa bam a cocin Living Faith dake Kaduna yace dan shi ba Kirista ne.

Hakan ya kawo karshen cece-kuce da Kiristoci a kafafen sadarwar suke yi akan cewar “matashin ba Kirista bane, hasa lima “sunan matashi Muhammad Sani.”

Mahaifin matashin ya tabbatarwa da Daily Trust cewar dan shi ba musulmi bane a yayin wata tattaunawa da jaridar tayi da Mista Ezekiel a gidanshi dake Marabar Demishi dake karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

Ya bayyana cewar dan nashi bai taba zama musulmi ko na kwana daya ba.

Ya kara da cewar an haifi Nathaniel a shekarar 1991 ya kuma yi karatu a jihar Kaduna inda ita mahaifiyarshi ta kasance mutuniyar Nassarawa ce.

Da yake amsa tambayar ko dan shi yana amsa sunan Muhammad Sani, ya bayyana cewar “A’a bai taba zama musulmi ba ko na kwana daya.

Karin Labarai

UA-131299779-2