Labarai

Mutane sun koma hawa Dawakai bayan gwamnati ta haramta ‘acaba’ a Legas

Mutane a kwaryar jihar Legas sun koma hawa Dawakai a matsahin abin hawa na zirga-zirga.

Hakan na zuwa ne bayan da gwamnatin jihar ta haramta haya da babura ciki har da masu kafa 3 a kwaryar jihar ta Legas.

Cikin wani bidiyo da ya baza gari, DABO FM ta tattara yadda aka ga Dawakai dayawa a kan titunan jihar da mutane a kai suna yawo.

Biyo bayan tattaunawa da wasu maganganu a shafukan sada zumunta, DABO FM ta tattara cewa haya akeyi da dawakan daga tituna zuwa titi.

Wasu bidiyoyin sun nuna tadda Dawakan suka galabaita bisa gajiya da ta kai ga sun kwanta a kan titi har basa iya tashi.

Karin Labarai

Masu Alaka

Buhari zai gina sabon dakin saukar fasinjojin jiragen sama a jihar Legas akan Naira Biliyan 14 – Minista

Dabo Online

Buhari zai jagoranci raba motocin zirga-zirga 820 a jihar Legas

Dabo Online
UA-131299779-2