Daliban Kwankwasiyya sun sauka a kasar Indiya

Dalibai 105 daga cikin 242 da gidauniyar Kwankwasiyya ta dauki nauyin karatunsu sun sauka a kasar Indiya.

Daliban dai sun sauka a filin tashi da saukar Jirage na Indira Gandhi dake birnin New Delhi, babban birnin kasar.

A jiya Talata dai akayi bankwana da daliban a jihar Kano, inda daga nan ne suka tafi jihar Legas, a nan ne suka hau jirgi zuwa hadaddiyar daular Larabawa kafin daga bisani suka sauka a kasar ta Indiya.

Mafiya daliban da suka tafi a jiya Talata, daliban Jami’ar Mewar ne dake jihar Rajasthan a Arewacin kasar Indiya.

Daliban zasu shafe awanni 9 da mintuna 56 kafin su isa makarantar da fara karatun nasu.

Masu Alaƙa  Gidauniyar Kwankwasiyya ta kai karin dalibai kasar Dubai da Sudan domin karatun digiri na 2

A gobe Alhamis ake sa ran tasowar a kalla wasu dalibai 50 zuwa kasar ta Indiya.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Engr Kwankwaso ya bayyana cewa; “Jirgin karshe na daliban zai tashi ne ranar Laraba, 2 ga watan Oktobar 2019.

Karin Labarai

Leave a Reply

Your email address will not be published.