Sharhi

‘Minista akayi yunkurin kashewa’ – Hakan ya sanya masa rigar Siyasa kenan?

Bayan zarge-zarge da shan suka da Jagoran darikar Kwankwasiyya da mabiyanshi suka sha, cece-kuce ya chanza salo.

Tin da fari dai wasu daga cikin mabiya Kwankwasiyyar suna gani cewa sunyi wa Dr Pantami ihun ‘Bamayi’ bisa dalilin kasancewar Malamin dan Siyasa mai rike da mukamin Minista a halin yanzu.

Inda a bangaren masu goyon bayan jami’iyyar APC da suke ganin cin mutunci ne ga malamin addinin Islama, duba da irin tarin Ilimin Al-Kur’ani da Hadisai wanda malamin ya tara, bai kamata ayi masa haka ba.

Sai gashi a wani yanayi, mabiyan jami’iyyar ta APC sun fito da sabon salon fitar da labaran a kafafen sada zumunta na cewar; “Yan Kwankwasiyya sunyi yunkurin hallaka Ministan Najeriya.”

Ko dai suma sun yardar cewa malamin ya shiga harkar siyasa ne? Tin da dama duk dan siyasa yasan masoyan gari duk ba nashi bane.

Zaku iya bayyana mana ra’ayoyinku a kasan wannan rubutun ko kuma ta shafinmu na Facebook a Dabo FM

Karin Labarai

UA-131299779-2