Labarai

Gidan Rediyon Freedom ‘Muryar Jama’a’ dake Kano ya cika shekaru 16 da fara watsa labarai

Gidan Rediyon Freedom dake jihar Kano ta cika shekaru 16 da fara gudanar da shirye-shirye daga shekarar 2003 zuwa 2019.

A yanayi wanda a iya cewa; Freedom Radio, itace tasha daya tilo mallakar ‘yan Najeriya da ta fara yada shirye shirye cikin harshen Hausa a fadin Najeriya.

Freedom Radio ta zamo allon misali ga dukkanin gidajen rediyo da aka bude bayar kafuwarta, kama daga tsarin gudanar da shirye-shirye dama kirkirar sabbin shirye shirye masu nishadantarwa, Iliminatarwa da fadakarwa.

A tarihin siyasar jihar Kano, gidan rediyon Freedom ya taka gudunmawa wajen baiwa kowa damar fadar albarkacin bakinshi musamman ga masu hamayya da gwamnati wanda kafin kafuwar tashar basuda muryar fadar ra’ayinsu duba da cewa gidan Rediyon Kano dake Bello Dandago, baya bada filin zukar gwamnati ko fadar ra’ayin da gwamnati bata bukata.

Shirin Kowane Gauta da Mallam Muhammad Sulaimanu Gama ya fara shiryawa, shine shiri na farko wanda kuma har yanzu ake kwaikwaya wajen yin shirin siyasa a kowacce gidan rediyo dake fadin jihar dama arewacin Najeriya.

Shirin Inda Ranka, shiri ne da gidan rediyon ta fara wanda ya chanza akalar yanayin labaran da mutane suka saba ji a rediyon Kano a cikin shirin ‘Taskar Labarai’ wanda ake ganin kamar bazasu taba yiwuwa ba.

Kadan daga cikin shirye-shiryen gidan rediyon Freedom da sukayi shiru tin daga fara gudanar kawo yanzu.

 • Allah Daya gari bam-bam
 • Barka da Hantsi
 • Birgimar Hankaka
 • Brainstorm Quiz
 • Hasken Makaranta
 • Inda Ranka
 • Kalubale
 • Kowanne Gauta
 • Mambarin Malamai
 • Mukyakyata
 • Taskira

Zuwa yanzu, tashar tana da reshen a jihar Jigawa da jihar Kaduna tare da kirkirar takwarar tashar Dala FM wanda hukumar Freedom Media Group dake gudanarwa.

Daga Dabo FM, muna mika sakon taya murna zuwa ga Freedom Radio.

UA-131299779-2