Wani dan Najeriya mai shekaru 25, dalibi dake karatu a kasar Indiya, ya mutu. Inda aka samu gawarshi a cikin gidan da yake zama dake unguwar Potheri a birnin Kattankulathur ta jihar Tamil Nadu a kudancin kasar Indiya.
Rundunar yan sandan jihar Tamil Nadu ta bayyana Okpe Victor a matsayin sunan dalibin, mazaunin jihar Kaduna a Najeriya. Hakazalika yana shekarar karshe a karatun da yake yi na Ilimin Kimiyyar Kwamfuta a wata jami’ar kudi ta garin Kattankulathur.
Jaridar The Hindu dake da shedikwata a birnin Chennai, ta rawaito cewar rundunar ‘yan sandan jihar sun bayyana cewar mahaifyar mamacin, Rosemary Okpe, tayi ta kiran dan nata bata sameshi ba. Daga bisani ta kira abokinshi domin ya duba mata Victor.
“Da zuwan abokin, yayi ta buga kofa ba a bude ba. Bayan ya leka ta wundo, ya hangi Victor a kwance.” – Kamar yadda wani jami’an yan sanda ya bayyana.
“Ya sanar da asibitin makarantar tare da ma’aikata domin a duba Victor, aka samu ya rasa ranshi. Daga nan aka sanarwa da jami’an tsaro.”
DABO FM ta tattara cewar har yanzu ba’a san musababbin mutuwar dalibin ba, sai dai rundunar ‘yan sanda tace tini ta aike da gawar Victor zuwa asibiti domin gano musababbin mutuwar.
Hakazalika DABO FM ta tattara cewar Victor ya kasance mamallakin shagon yanar gizo-gizo na Aikart dake siyar da kayayyakin sawa.
