Labarai

Dangote zai dauki daliban Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano ‘KUST’ aiki kai tsaye

Shugaban kamfanin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote, ya rattabawa hannu ba tare da bata lokaci ba kan aminta da daukar daliban jami’ar KUST aiki a kamfanonin da yake jagoranta tare da wasu alfanu don cigaban jami’ar.

Farfesa Shehu Alhaji Musa, shugaban jami’ar Kimiyya da Fasaha dake Kano ne ya bayyana haka a shafinshi na Facebook jim kadan bayan wata ganawa da hukumar makarantar tayi da Aliko Dangote a jihar Legas.

DABO FM ta binciko cewa daliban da suka kammala karatu a bangaren Noma, ‘Engineering’ da ‘Architecture’ zasu samu aiki kai tsaye a karkashin kamfanonin Dangote.

Sai dai Farfesa Shehu ya ce; “Daliban da suka fita da sakamakon Digiri mai lamba ta daya da Lamba ta biyu ‘First da Second Class Upper’ ne zasu ci gajiyar wannan shirin.

“A tattaunawarmu da Alhaji Aliko Dangote GCON, yayi alkawarin aiwatar da dukkanin alkawura da ya daukarwa KUST.”

“Tini ya turo da Injiyoyi don fara aikin wutar Lantarkin da zata samar da wuta mai yawan 33KVA a Jami’ar.”

“Ya rabbataba hannu kan aiwatar da ayyuka ba tare da bata lokaci ba kamar haka:

  1. Daukar Farfesohin kasashen waje guda 15.
  2. Ginin Gidajen Farfesoshi guda 15.
  3. Kawo Na’urar bada hasken lantarki mai karfin KVA 1000.
  4. Ginin na dindin-din ga hukumar gudanarwar jami’ar.”

DABO FM ta tattaro cewa Alhaji Aliko Dangote yayi alkawarin gyaran dakunan kwana na ‘yan mata wanda yayi gobara tare da taimakawa wajen bunkasa fannin sana’o’in da tallaffin ga matasa domin dogaro da kawuna.

Karin Labarai

UA-131299779-2