Labarai

Uwargidan gwamnan Anambra ta je taron ta’aziyya sanye da tabarau na Naira miliyan 1

Uwargidan gwamnan jihar Anambra, Misis Ebelechukwu Obiano ta sanya tabarau na dalar Amurka 2,755.

Uwargidan gwamnan ta halarci taron binne mahaifin shugaban kamfanin jirgin Air Peace, Chief Micheal Chukwuka Onyema.

Misis Obiano tana daga cikin manyan mutanen da suka samu damar halarta taron binne mamaci da aka gudanar a dakin bauta na St Patrick Katolika a Mbosi, Ihiala dake jihar ta Anambra.

Jaridar Punch ta tabbatar da cewa Uwargidan gwamnan, Misis Obiano, masoyiyar sanya tabarau ce a koda yaushe.

Hakan yasa DABO FM ta gudanar da bincike dangane da tabaran da uwargidan gwamnan ta sanya.

Tabarau mai suna ‘Swarovski Crystal’ wanda kamfanin Gucci yake yi, yana da daraja ta gaske.

Farashin shi a shagunan yanar gizo-gizo yana kaiwa Naira 995,932.50 zuwa miliyan 1 a kudin Najeriya, wanda a hakan ma babu kudin dako daga kamfanin gilashi zuwa gidan wanda ya siya.

Ga hotunan gilashi a shafin dake dillancinshi dake kasar Amurka;

Daga shafin tillanci na GUCCI dake kasar Amurka.

Karin Labarai

Masu Alaka

An fara gano dattawan dake zancen batsa da matar data caccakawa mijinta wuka

Dabo Online

Sarakuna 5, Hakimai 33 da Sojoji 10 keda hannu dumu-dumu a kashe-kashen Zamfara -Kwamatin Bincike

Muhammad Isma’il Makama

Wani malami a babbar makaranta dake kano ya amsa laifin haike wa dalibarsa

Muhammad Isma’il Makama

Agwaluma na rage karfin maza -Binciken Masana daga Jami’ar Madonna

Muhammad Isma’il Makama

Yanzu Yanzu: EFCC ta cafke Sanata Shehu Sani

Muhammad Isma’il Makama

Buhari ya bada umarnin kubutar da dan Najeriya dake jiran hukuncin kisa a Saudiyya

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2