Tue. Nov 19th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Jami’ai sunyi kame ‘Dan gwagwarmayar Kwankwasiyya’, Abu Hanifa Dadiyata

2 min read

Wasu jami’a dauke da makamai, wadanda ake kyautata jami’an SSS ne sun kama Abu Hanifa Dadiyata a gidanshi dake jihar Kadunan Najeriya.

Mai magana da yawun dan takarar gwamnan jihar Kano a jami’iyyar PDP, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fita.

DABO FM ta rawaito cewa; Dawakin-Tofa yayi kira ga hukumar ta SSS da su dawo da Dadiyata cikin koshin lafiya ba tare da yi masa wani lahani ko taba lafiyarshi ba.

“Daga rahotannin da muke samu, a daren jiya, wasu jami’ai dauke da manyan makamai wadanda ake zaton jami’an DSS ne, sun kama Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Abu Hanifa Dadiyata a gidanshi dake Kaduna.”

“Dadiyata shine wanda yake ja gaba a manhajin Twitter wajen kare muradin darikar Kwankwasiyya a arewacin Najeriya.” -Kamar yacce sanarwar tazo dashi.

Dadiyata dalibi ne dake karatu digirin-digirgir a jami’ar kasar Malaysia, inda kuma yake Malamin Jami’a.

DABO FM ta tattaro cewa Abu Hanifa Dadiyata, yana da aure tare da ‘yaya.

“Muna kira ga jami’an tsaro da su saki Abubakar Dadiyata ba tare da ji masa rauni ko raunana lafiyarshi ba.”

A matsayin na masu hamayya da gwamnatin jihar Kano dama Najeriya, zamu cigaba da yin sukarmu bisa tsarin doka.”

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.