Attahir Bafarawa

Rikicin Kano zai iya shafar Masarautun Arewa – Attahir Bafarawa

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahir Bafarawa ya ja hankalin cewar rikicin kirkirar sabbin masarautu a jihar Kano ka iya shafar shafar sauran masarautun jihohin arewacin Najeriya.

A yayin wata hira da tsohon gwamnan yayi da sashin Hausa na Muryar Amurka, DABO FM ta tattaro tsohon gwamnan yana bayyana cewa lallai sarauta zata lalace idan ana yi wasu masarautun.

Yace; “Maganar ayi masarautu a Kano ba ta ko taso ba, in dai ana haka, sarauta za ta lalace a Arewa.”

Ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ne kadai zai iya shawo kan lamarin a matsayinshi na shugaban kasa kuma dan Arewa.

Shima a nashi bangaren yace baya goyon bayan rarraba masarautun kuma bai kamata a siyasantar da sarauta ba musamman irin ta jihar Kano.

Masu Alaƙa  Masarautar Rano ta hukunta Hakimai da sukayi wa sarkin Kano Sunusi mubaya'a

Yace; “Bai kamata azo ana wasa ana sa siyasa a masarauta irin ta Kano ba.”

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.