Daurin shekaru 2 da tarar N400,000 ga mijin da ba ya cin abincin matarsa

Karatun minti 1

Shugaban hukumar muzanta bil adam da taimakawa wanda aka dannewa hakki na Centeral Region dake kasar Ghana, Sufuritanda George Appiah-Sakyi yaja kunne mazaje a kan kin cin abincin matayen su.

Rahoton da Dabo FM ta tattara ya rawaito Sufiritanda George ya bayyana hakan babban lefi ne da ake kiran laifin da ‘Emotional Abuse’, wanda kuma aka kama da laifin kan iya tsintar kansa a gidan yari harna tsahon shekara 2.

Appiah ya kara da cewa bayan haka kuma tare da tarar zunzurutin kudi har Cedi na kasar Ghana GhC6000, wanda a kwatankwacin kudin Najeriya ya kai Naira dubu dari hudi.

Haka kuma ya bayyana cewa maza masu kaiwa dare ma na iya morar wannan hukunci, dama masu dukan matansu.

Daga karshe ya yi kira da duk matar da mijin ta yaki cin abincinta ta kai kara caji ofis mafi kusa. Kamar yadda My Ghana News ta fitar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog