Labarai

Daurin shekaru 3 a Gidan Yari ne hukunci fasakaurin buhun Shinkafa daya tak – Hameed Ali

Hukumar hana fasakauri ta Kwastam ta bayyana hukuncin daurin shekaru 3 a gidan yari ga duk wanda aka kama yayi fasakurin buhun Shinkafa daya zuwa Najeriya.

Shugaban hukumar, Kanal Hameed Ali ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da mutanen dake rayuwa a kan iyakar Najeriya da Nijar a karamar hukumar Mai Gatari ta jihar Jigawa.

DABO FM ta tattaro cewa shugaban ya bayyana cewa shigowa da kayayyakin da gwamnati ta haramta yana matukar tasiri wajen karya tattalin arzikin Najeriya.

“Gwamnatin tarayya tana matukar kokari wajen bunkasa noman Shinkafa a Najeriya, amma yin fasakaurin Shinkafar kasar waje yana kawo nakasu ga kudirin da shirin Gwamnatin.”

“Yawancinku, ku ne kuke shigowa da Shinkafar a kan baburanku.”

“Babu sassauci ko daga kafa, duk wanda aka kama, za’a hukuntashi bisa tsari, kuma zaman Gidan Yari na shekara 3 ne a duk buhun Shinkafar da aka kama mutum ya shigo da ita.”