Labarai

CBN zata dauki dukkanin ‘yan jihar Ebonyi masu matakin ‘First Class’ a Economics aiki

Babban bankin Najeriya, CBN, ya sanya hannu kan daukar dukkanin ‘yan jihar Ebonyi wadanda suka kammala karatu da matakin ‘First Class’ a bangaren ‘Economics’ aiki kai tsaye.

Kwamishinan yada labaran jihar, Uchenna Orji ne ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin da yake bayyanawa manema labarai abinda aka aiwatar a zaman Majalissar Zartawar jihar.

Kwamishinan ya kara bayyana cewa gwamnan jihar David Umahi, ya yaba matuka da yacce babban Bankin yake taimakawa wajen habbakar tattalin arzikin mutanen jihar.

Haka zalika DABO FM ta tattaro kwamishinan ya kara bayyana cewa; Tini dai babban bankin CBN, ya sanya hannu kan fitarwa da jihar bashin Naira biliyan 2 wanda zasu biya da ribar kaso 2 na cikin kudin kacal idan sun tashi mayarwa.

Yace gwamnatin jihar zatayi amfani da kudaden wajen rarrabawa marasa karfi, masu kananan sana’o’i, kananan ma’aikatan gwamnatin da masu sana’o’in hannu. –Kamar yacce jaridar Daily Trust ta tabbatar.

“Kudaden zasu shigo ta bankin Zenith wanda muka tabbatar da zasu shiga hannun wadanda aka tsara a karkashin ma’aikatan raya al’umma.”

“Bisa ga yacce gwamnan ya tsunduma cikin sha’anin babban bankin, CBN ta sanya hannu domin daukar dukkanin yan jihar wadanda suka kammala karatu a sashin ‘Economics’ da matakin ajin Digiri na farko.”

“Saboda haka tin daga yanzu, duk dan jihar Ebonyi da yake da ‘First Class’ a ‘Economics, ya zama ma’aikacin babban bankin Najeriya kai tsaye.”