Labarai

Nagarta: Gwamnan Bauchi ya mayar wa UNICEF rarar kudin tallafin ciyarwa data baiwa jihar

Gwamnatin jihar Bauchi ta mayar wa UNICEF rara kudi na miliyan 15 da ta baiwa jihar domin yakar rashin cin abinci mai gina jiki.

Gwamnan jihar, Bala Muhammad ne ya rabbata hannu kan mayar da kudaden zuwa ofishin UNICEF na jihar Bauchi.

DABO FM ta tattaro cewa gwamnan ya sanya hannu ne a dai dai lokacin da yake ganawa da shuwagabannin UNICEF karkashin jagorancin Mista Bhanu Pathaki.

Gwamnan ya sanya hannun ne bayan da UNICEF ta shigar da bukatar neman gwamnatin ta dawo mata da kudaden da ba’ayi amfani dasu ba lokacin da aka gudanar da shirin a fadin jihar.

Bala Muhammad, ya kara bayyana rashin jin dadinshi bisa yacce tsohuwar gwamnatin jihar ta kashe Naira miliyan 732 ba tare da kyakkyawan tsari ba.

Ya kuma jaddada cewa; gwamnatin tashi zata cigaba da kokarin ganin cewa an kashe kudaden tallafi da jihar take samu ta hanyoyin da suka dace.

Comment here