Ball lokacin Lockdwon -KAno
Labarai

Dokar hana fita ta zama lokacin buga Kwallo tsakanin Matasa a unguwannin Kano

Duk da dokar hana fita da gwamnatin Dr Abdullahi Ganduje ta sanya a jihar Kanoidomin dakile cutar Koronavirus, matasan jihar sun bijirewa dokar hana fita a jihar..

A wani kwarya-kwaryan bincike da DABO FM ta gudanar, mun tabbatar da cewa matasa sun bijrewa dokar hana fita a cikin unguwanninsu musamman wadanda suke a tsakiyar birnin Kano.

DABO FM ta tabbatar da cewa, mafi yawancin cikin unguwannin birnin Kano, matasa ne suke holewarsu da buga Kwallon kafa.

Tare da hotuna da wasu bidiyo da zamu wallafa, zaku ga yadda ake cigaba da gudanar da ayyukan yau da kullin a unguwannin birnin Kano.

Fara wa da karamar hukumar Dala, DABO FM ta leka kan titin Dala Kan Tudu, inda ake gudanar da rayuwa kamar kullin, duk da cewa da mafi yawan shagunan dake titi a cikin unguwar a kulle suke.

Yayin da ake tsada da wasan Kwallo.

A unguwar Dambazawa, DABO FM ta ga wasu dandazon matasa da kananan yara suna buga kwallo cikin cunkuson tayar da hankali.

Latsa domin kallon bidiyon.

Wani mazaunin unguwar Fagge a jihar Kano, ya bayyana mana cewar ana cigaba da gudanar da harkokin yau da kullin a unguwar, kama daga zaman majalissa, buga kwallo da sauran harkoki.

“Jiya dai ‘yan sanda sun zo, amma kowa yana harkokinshi. Nima yanzu zan tafi majalissar da muke zama ta hira a kan kwana.”

A cikin wani bidiyo da Abba Hikima, wani lauya dan asalin unguwar Fagge ya wallafa a shafinshi na Facebook wanda ya tabbatar da bijirewa dokar hana fita, DABO FM ta tabbatar da bijirewa dokar da mazauna unguwar sukayi yayin da a bangare guda ake buga Kwallo a kan titunan unguwar.

Idan ba a manta ba, a jiya Juma’a, wani limami a unguwar Gwammaja ta jihar Kano, ya jagoranci sallar Juma’a a masallacin Isa Kafinta dake karamar hukumar Dala a jihar Kano.

Karin Labarai

UA-131299779-2