0
Mutane 10 sun sake kamuwa da Covid-19 a jihar Kano.
Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta tabbatar da sake samun mutanen a ingantaccen shafinta na Twitter.
“A halin yanzu, karfe 10:48 na dare, an sake samun masu dauke da Coronavirus guda 10 a jihar Kano.
Jumillar masu dauke da cutar a Kano ya zama 37, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta jihar KAno ta tabbatar.
An samu jumillar masu dauke da ciwon guda 542 a fadin Najeriya.
