Labarai

Yanzu- Yanzu: Ganduje ya tsige kwamishanan Kano ‘Mai Katobara’ bayan nuna farinciki da mutuwar Kyari

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya tsige kwamishinan ayyuka da gidaje na jihar Kano, Engr Muazu Magaji Dan Sarauniya. Ganduje

Hakan na zuwa ne bayan da kwamishinan ya bayyana farin cikinshi da mutuwar Mallam Abba Kyari.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Muhammad Garba ne ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar da ranar yau.

Sanarwar tace gwamnatin ta sauwake wa kwamishinan bisa saba dokar aiki.

Haka zalika tace a matsayinshi na ma’aikaci bai kamata ya rika shiga dukkanin wasu ayyuka da zasu rage darajar aiki ko wadanda basu kamata ba.

Korar na zuwa ne awanni kadan bayan DABO FM ta wallafa yadda kwamishinan ya yi kalamai masu tarin yawa na nuna farinciki da mutuwar tsohon shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayyar Najeriya, Mallam Abba Kyari wanda cutar Koronabairas ta zama ajalinshi.

Karin Labarai

Masu Alaka

Tsohon kwamishinan Kano da ya yi murnar mutuwar Abba Kyari, ya kamu da Koronabairas

Dabo Online

Kwamishina ‘Mai Katobara’ na Ganduje ya nuna jin dadi da mutuwar Abba Kyari

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2