(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Dokin Gaskiya: Bani da Masaniya akan Lauyoyi 100 da akace zan jagoranta domin kare Abba K Yusuf a Kotu – Barr Bulama Bukarti

dakikun karantawa

Fitattecen dan gwagwarmaya kuma Lauya mai rajin kare hakkin dan Adam, Barr Audu Bulama Bukarti, yace bashida masaniya akan rubutun da ake yadawa na cewa zai jagoranci lauyoyi dari zuwa Kotu akan ganin cewa anyi mutanen Kano adalci a zaben Gwamna da aka gudanar a jihar Kano.

Ga dai yacce Barr ya wallafa a shafinshi na sada zamunta, Facebook.

“Tun jiya gomman abokai da masoya ke tuntu6a ta ta kafafen sadarwa daban-daban game da labarin da ke yawo cewa zan jagoranci lauloyi 100 wajen kwato hakkin mutanen Kano game da fashi tsakar rana da aka yi musu ranar asabar da ta gabata. Da yawa kuma sun turo min addu’o’i masu kyau da maganganun karfafa gwiwa. Yanzu har manyan Kano sun fara kira na akan maganar. Nagode sosai, saidai kuma akwai magana.

A haqiqanin gaskiya wannan labari ba haka yake ba. Ban san maganar ba kuma ba’a yi ta da ni ba. Ban san inda maganar ta samo asali ba. Na so ace da ni za’a yi Shari’a tunkude wannan mutumin amma kash hakan ba zai yiwu ba domin kuwa yanzu ba na kasar.

Amma ina kyautata zaton cewa ita jam’iyyar da aka zalinta tana da kwararrun lauyoyin da za su yi tsayin daka wajen gudanar da wannan aiki. Kuma ina da karfin gwiwar cewa Allah zai taimake su domin Ya haramtawa kanSa zalinci kuma Ya haramta shi gare mu. Abinda aka yi Kano ranar Asabar fashi ne da tsabagen rashin kunya da tsatsar zalinci da tsagwaron tsaurin ido.

Hirar da na ji jagoran marasa kunyar da suka yayi a gidan radiyon BBC shi ya kara tabbatar min cewa wannan mutumin bai dace da shugabancin ko na dabobi ba, bare mutanen Kano masu daraja. Bayan rashin ta’idon da suka tamka, ya kuma fito ya gawaya duniya maganar da ya san karya ce kuma duk wanda ya gani ko ya karanta ko ya samu labarin abinda ya faru ya san karya ne. Ga cin amana, ga zalinci, ga karya. Ai wannan abu yayi yawa wai maye da hauka.

Ina roqon Allah Ya raya mu mu ga ranar da za’a kure wannan rami na karya, a bawa masu hakki hakkinsu. Allah kuma Ya kaimu zaben 2023 domin a tamkawa jam’iyyar ta kitsa wannan abu littafinta a hannun hagu.

Audu Bulama Bukarti
27/03/2019

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog