Al’umma karamar hukumar Fagge sun zargi dan gidan tsohon kakakin majalissar jihar Kano, Hon Yusuf Abdullahi Ata da aikata wa wata baiwar Allah danyen aikin da yayi sanadiyar rasa idonta na hagu, duk a cikin murnar cin zaben Dr Abdullahi Ganduje.
An zargi yaron da aka fi sani da Bilal Yusuf Abdullahi Ata, ya jefa “Knock-Out” gidan su budurwa bisa kasancewar su ba mabiya ra’ayin gidan tsohon kakakin bane, duk da kasancewarsu makota a cewar wasu mazauna unguwar da suka zanta da DABO FM.
DABO FM ta tattara cewa Bilal Yusuf Ata nada shekaru 21 kacal a duniya.
Yanzu haka dai Budurwar mai suna Na’ima Sani Lawan tana kwance a asibitin Murtala dake kwaryar cikin birnin Kano.

Sai dai daga rahotanni da muke samu, jama’ar unguwar sun koka kan yadda babu wani daga gidan tsohon kakakin da ya zo yi musu jaje balle bayar da dauki.
Hasali ma an zargi Rt Hon Yusuf Abdullahi Ata da yin hanzari wajen daukar dan nashi daga kasar Najeriya zuwa kasar Saudi Arabiya.
Mun yi kokarin jin ta bakin bangaren biyu, har yanzu bamu samu kowanne a ciki ba. Sai dai muna cigaba da kokari.
“Tin ba yau ba daman ake samun irin wadannan matsalolin a cikin unguwar Fagge, daga kan ‘yayan Hon Abdullahi Ata, da S.A Ali Baba Agama lafiya.” – Cewar wani mazaunin unguwar da ya nemi a sakaya sunanshi.
A kwanakin da suke kasa da mako daya, an hangi ‘yayan S.A Alibaba, sun fito kan tituna a Fagge, suna cin mutunci mutane tare da fadar bakaken magangani da taken “Ana mana bakin ciki.”

