Hajj2019: Kada jama’a su yadda da kudin aikin Hajjin 2019 da ake turawa a Social Media – Hukumar Alhazai

Karatun minti 1

Hukumar jin dadin alhazai tayi kira ga al’ummar Najeriya da kada su yadda da karairayin da ake yada wa akan kudin hajjin bana na shekarar 2019.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Babban mai gudanarwar hukumar ta kasa, Ibrahim Muhammad yace, jiya sun gano yadda aka rika yada kudin aikin Hajjin shekarar 2019. Ya kira da wannan labarin “Karya” tare da rashin tushe.

Yace ana yada cewa Naira Miliyan daya da dubu dari takwas (N1.8M) shine kudin aikin Hajji ta bana.

Muhammad, yayi gargadi ga mutane su guji yada labaran karya, tinda Al-Qurani ma yayi magana akan masu aikata laifin yada karya, kuma sunada babban hukunci a gurin Allah.

“Mun rasa gane ta ina masu yada kudin Hajji suka samu wannan labari, domin Har yanzu hukuma bata kayyade kudin Hajjin ba.”

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog