Labarai

Dr Mudi Spikin: Shekaru 7 da rashin cikon karshe na mahalarta taron yancin Najeriya a Landan

A cikin makon da muke ciki ne daya daga cikin jagororin Arewa, Dr Mudi Spikin zai cika shekaru 7 da mutuwa tin bayan rasuwarshi a jihar Kano.

DABO FM ta tattara cewar Dr Mudi Spikin ya rasu ne a ranar Talata, 19 ga watan Fabarairun 2013 a gidanshi dake karamar hukumar Fagge a birnin Kano, ya bar duniya yana da shekaru 83.

Kafin rasuwashi ya kasance daya daga cikin iyayen Najeriya wadanda suka samu halartar taron da aka fara tsara karbar mulkin Najeriya daga hannun turawan mulkin mallaka na kasar Burtaniya wanda aka gudanar a birnin Landan a shekarar 1953.

Mutuwar Dr Mudi Spikin a 2013, ta kawo karshen rayuwar dukkanin wadanda suka wakilci Najeriya a taron Landan na 1953, shekaru 7 kafin baiwa Najeriya ‘yancin kai.

A bangaren kafa jami’iyyar NEPU, Dr Mudi Spikin, ya kasance daya daga cikin iyayen da suka kirkiri jami’iyyar NEPU wadda suka tashi tsaye wajen kwatowa talaka yancin gudanar da rayuwa cikin aminci daga hannun ‘shafaffu da mai’ na wancen lokaci.

Bayan tattauanawa da wasu daga cikin ‘ya’yan mamacin tare da ziyartar gidashi na unguwar Fagge, DABO FM ta tattara cewar Dr Mudi Spikin, ya gudanar da rayuwarshi bisa koyarwar addinin Islama tare da taimakon al’umma kuma ya kasance mutum ne mai son fiyayyen halitta har a wata wakarshi yana cewa;

Kullum na tashi da safiya,

Sai na tuno shi (Annabi Muhammad SAW) a zuciya,

Inyi murmushi in yi dariya,

Wata ran a hanya ni daya,

Sai ga shi na dau dariya.

Ba dariyar komai bace,

Murnar ina kaunarsa (Annabi Muhammad SAW) ce,

Wannan fa kyautar Rabbi ce,

To ni a yau me za ni ce?

Sai dai kawai in yi godiya.

Da uwa da ‘yata har uba,

Na bashi ba wata fargaba,

Duk nawa komai na raba,

Shin me yasa ne zan raba?

Na bashi duk baki daya.

Tun babu kas kuma ba sama,

Tun can azal aka girmama,

Darajarsa tun can an gama,.

Kai dan uwa bar gardama,

Dubo cikin Ishriniya.

Kufa lura waye yai yashi?

Dukkan halitta ba i’shi,

Na gaskata wallai da shi,

Ai sai mu tashi mu gai da shi,

Don girmamawar gaskiya.

Allah dada masa daukaka,

Sannan kaza daraja duka,

Alai Sahabbai duka,

Matansa ‘ya’ya duka,

Allah ka ba su gaba daya.

Mudi Spikin naku ne,

Wannan irin wakensa ne,

Ni naku ku nawa ne,

Duk ayyuka na jingine,.

Sai nayi murnar godiya.

Mudi Spikin ‘1950’

Marigayi Spikin, Fasihi kuma haziki a fannin waken Hausa wanda a yanzu haka ana karantar da wakokinshi a wasu jami’o’in Najeriya.

Ku kasance damu a ranar Laraba, 19 Fabarairu domin samun tarihi da wasu baitukan wakokin fasaha da ilimi na mamacin.

Da wannan muke amfani da wannan dama wajen sake mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalan Dr Spikin.

Karin Labarai

UA-131299779-2