Labarai

Duk da dokar hana fita, an gudanar da Sallar Juma’a a Kano

Duk da dokar hana fita da ta fara aiki a jihar Kano ranar Alhamis da misalin karfe 10 na dare, anyi Sallar Juma’a a wani masallaci dake cikin birnin jihar ta Kano kamar yadda zaku gani a bidiyon kasa.

DABO FM ta tattara cewar an yi sallar ne kamar yadda aka saba, inda sahu ya fito har wajen gaban gidajen al’ummar unguwar Gwammaja dake karamar hukumar Dala ta jihar Kano.

Wani shaidar gani da ido mazaunin unguwar Gwammaja ya shaidawa DABO FM cewar mutane daga sassan karamar hukumar Dala sun halarci wannan masallacin.

“Ina zaune a kofar gida naga mutane suna ta wucewa zuwa masallacin Isa Kafinta, wasu da sallaya wasu babu.”

Haka zalika DABO FM ta tabbatar da masallacin mai sunan Masallacin Isa Kafinta, yayi cikar dango inda aka rika hangen mutane da daddumar sallah su na ta kai koma domin samun sallar cikin jami’i.

Sai dai a wani faifan bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta, an hangi jami’an tsaro sun je masallacin domin kama limamin da ya jagoranci sallar Juma’a ta yau.

Zuwa yanzu da muke hada wannan rahoton, muna tuntubar kakain rundunar yan sandan jhihar Kano, DSP Haruna Kiyawa domin jin yadda ta kasance.

Zamu bayyana muku yadda mukayi da shi nan gaba kadan.

Karin Labarai

Masu Alaka

Tirkashi: Masu dauke da cutar Koronabairas sun yi garkuwa da ma’aikatan lafiya a Kano

Muhammad Isma’il Makama

Mutumin da cutar Koronabairas ta fara kamawa a Kano ya warke

Dabo Online

Ganduje ya sassauta dokar hana fita a Kano

Dabo Online

Yanzu-yanzu: Mutane 12 sun sake kamuwa da Kwabid-19 a Kano, jumilla 21

Dabo Online

Gwamnatin Kano ta kara tsawaita dokar hana fita

Dabo Online

Yanzu-yanzu: Mutane 2 sun sake kamuwa da Covid-19 a Kano, jumilla 3

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2