Home Kiwon LafiyaYanzu yanzu: An samu karin mutane 51 masu dauke da Coronavirus, jumillar 493 a Najeriya

Yanzu yanzu: An samu karin mutane 51 masu dauke da Coronavirus, jumillar 493 a Najeriya

by Dangalan Muhammad Aliyu
0 comments

Hukumar dake kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC ta sake tabbatar da samun karuwar masu dauke da cutar Covid-19 guda 51 a daren Juma’a .

Kamar yadda hukumar ta bayyana a shafinta na yanar gizo gizo da shafin Twitter, tace adadin wadanda aka tabbatar a Najeriya ya zama 493.

“A yau da misalin karfe 10:10 na dare an sake samun masu dauke da cutar ‘Corona Virus’ guda 51. An samu guda 32 a Lagos, 6 a Kano, 5 a Kwara, 2 a Abuja, Oyo da Katsina sai guda 1 a jihohin Ogun da Ekiti.”

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00