(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Duk malamin daya taba mu sai munci masa mutunci – Sanata Kwankwaso

Karatun minti 1

Tsohon gwaman jihar Kano, Engr Dr Rabi’u Musa Kwankwaso yace malamai su shiga taitayinsu wajen yin kalaman batanci akan wani ra’ayi na harkar siyasa da sukeyi.

Maganar data fito daga wani shiri mai suna Abba Gida Gida wanda gidauniyar Kwankwasiyya take daukar nauyin saka shirin a Dala FM 88.5 dake birinin Kano.

“Dayawa daga cikin wadannan malamai nasansu, nasansu asalinsu, nasansu akan irin laifuffuka manya-manya da sukayiwa al’umma kuma sukewa Allah, wadannan mutane sun shafawa kansu toka saboda neman abin duniya wanda dama tsarinsu ya tafi akan neman duniya , suna tafiya suje su nemo kwangila abasu kudade domin fadar karya da son zuciya.

Babbar magana itace, idan malami ya fadi abubuwa na sukar wani wanda mukeso, kar kayi mamaki kuma idan muka tashi muma zamuyi amfani da damarmu, idan shi yayi da labarci, mu kuma in muka duddura masa ashariya, ko musa yaranmu su ci masa mutunci.”

Wasu daga cikin kalamai Sanata Rabi’u Kwankwaso kenan.

Ki cigaba da kasancewa damu domin kawo muku maganar kamar yacce take domin sauraro.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog