Labarai

Masu ruwa da tsaki sun dauki aniyar dai-daita rikicin shugabancin karamar hukumar Zaria

Wasu dattijai masu kishin karamar hukumar Zariya da ke Jihar Kaduna, karkashin jagorancin kungiyar ci gaban waje, wato Waje District Development Association, WDDA. sun fara kokarin sasanta rikicin da ya kunno kai tsakanin bangaren dokoki da na zartaswa a karamar hukumar.

Zaman da masu ruwa da tsakin suka fara, ya fara ganawa ne da bangaren dokoki domin jin musabbabin rikicin da ya taso, wanda har ta kai ga yunkurin tsige shugaban karamar hukumar Injiniya Aliyu Idris Ibrahim.

Dakta El-Harun Muhammad, daya ne daga cikin wanda suka jagoranci zaman, ya shaidawa Dabo FM cewa, a matsayin su na dattijai kuma masu ruwa da tsaki, ba zai yiwu su zura ido abubuwa na naiman tabarbarewa ba, ta yadda aka jima ana musayar zafafan kalamai musamman a kafafen yada labarai.

Ya ce, taron nasu sam babu batun siyasa ko bangarenci a ciki, Kawai suna da manufar gyara abubuwan da suka lalace ne ta yadda jama’a za su ci gaba da amfanuwa da romon damokradiyyar da gwamnati ke kawowa Al’ummar ta.

A cewar Dr El-Harun Muhammad, Zariya na da muhinmanci matuka tsakanin sauran kananan hukumomin fadin najeriya, don haka dole ne Al’ummar da ke cikin ta su tsayu domin samun ci gaban ta.

Kadan daga cikin matakin da su za su bi domin samun wannan maslaha shi ne, ganawa da bangaren zartaswa wato bangaren shugaban karamar hukumar Injiniya Aliyu Idris Ibrahim da bangaren gwamnatin Jihar Kaduna.

Daya daga cikin mahalarta taron Malam Ishaq Alhassan Kauran Mata, ya roki duka bangarorin su maida wukan cikin kube kuma su dakatar da shiga kafafen yada labarai barkarai domin samun nasarar sulhun nasu.

Idan dai za’a iya tunawa, a farkon makon da muke ciki, Dabo FM ta bada labarin wasu fusatattun Kansilolin karamar hukumar Zariya su 11 suka sanya hannu domin tsige shugaban karamar hukumar Injiniya Aliyu Idris Ibrahim daga mukamin sa, duk da daga bisani, 4 daga cikin su sun janye daga sanya hannun da suka yi.
Yanzu dai adadin Kansiloli 7 ne cikin 13 suka doge akan matsayin su na tsige shugaban karamar hukumar, yayin da 6 ke goyon bayan sa.

Masu Alaka

Rikici ya barke a zauren majalisar Kansilolin karamar hukumar Zaria

Mu’azu A. Albarkawa

Zaria: Kansilolin da suka sanya hannun tsige shugaban karamar hukumar sun janye

Dabo Online

Har yanzu shugaban karamar hukumar Zaria da Kansiloli suka tsige bai sauka ba

Dabo Online
UA-131299779-2