Duk wanda ya shigo da kaya na sama da N50,000 Najeriya, zai biya haraji – Kwastam

Rundunar Kwastam ta ce tana tunatar da ‘yan Najeriya masu tafiye-tafiye a jirgin sama cewa; Zasu biya haraji yayin shigowa da kayan da darajar su ta wuce N50,000.

DABO FM ta tattara cewa, rundunar ta kara jaddada cewa kayan da darajarsu take kasa da N50,000 ne kadai zasu wuce ba tare da sun biya haraji ba.

Kakakin rundunar, DC Joseph Attah, ya bayyana haka tare da fadar korafi da bukatuwar da ‘yan Najeriya sukeyi ta a kara darajar kayan daga N50,000.

Sai dai DC Joseph ya baiwa ‘yan Najeriya hakuri tare da jaddada cigaba da wanzar da dokar har sai masu ikon chanza dokar sun yi mata gyara.

Masu Alaƙa  Custom zata kashe Biliyan 3.1 kudin share-share, 128m na kallon 'Tv', 78m na 'Photocopy'

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.