Labarai

An samo wani mutumin Kano a raye bayan ya nutse a ruwa shekaru 30 da suka wuce

Aminu Baita shine mutumin da ya fada teku shekaru 30 da suka wuce, wanda har aka dauka ya mace tun a shekarar 1990, cikin ikon Allah an same shi a raya harma ya hadu da iyalinsa.

A ta bakin wani dan uwa a gareshi, Yakubu Musa yace Malam Baita dai kafin bacewar sa ma’aikacin lafiya ne, inda daga bisani ya samu tabin hankali a karamar hukumar Dambatta kimanin kilo mita 70 daga cikin birnin kano.

Da yake bayyana al amarin kamar almara cikin farin cik Yakubu ya kara da cewa “Dan uwana ya dawo bayan ya mutu” Ya ci gaba da bayani, “Malam Baita ma’aikacin lafiya ne mai kwazo da yake aiki karkashin ma’aikatar lafiya ta jihar Kano.”

“Yayi aure cikin farin ciki kafin daga bisani ya fara wasu abubuwa da suke nuna ya samu tabin hankali, yazo ya rasa aikinsa tare da auren sa baki daya, daga nan ya tsinci kansa a wajen kula da masu matsalar tabin hankali dake dambatta.”

“Daga nan ne ya samu ya fice wata rana inda a ka ce ya fada ruwa yayi iyo, wannan iyon ne bamu kara ganin sa ba, abin mamaki wani babban yayanmu yaje neman sirikin sa a karamar hukumar Toro dake jihar Bauchi, bai sami sirikin nasa ba sai yaci karo da dan uwan sa Aminu.”

Karin Labarai

Masu Alaka

An kama Jirgin sama cike da kudi a jihar Kano

Dabo Online

Bincike ya nuna Ƴan Majalisar Tarayya na Kano ɗumama kujera suke a Habuja

Muhammad Isma’il Makama

Makarantu a garin Garo dake jihar Kano na cikin halin ko-in-kula

Muhammad Isma’il Makama

Dama can nasan Ganduje ne yaci zaben Kano -Buhari

Muhammad Isma’il Makama

Hon Sha’aban Sharada zai tura Dalibai 100 zuwa kasashen Waje yin Digirin farko

Dabo Online

Yanzu-Yanzu: El-Rufa’i ya bawa Sanusi II Murabus babban mukami, kwana 1 da sauke shi

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2