Boko Haram: A jihar Borno kadai, mutane sama da dubu 140 ne suka yi gudun Hijira a shekarar 2019

Dubban mutane ne suka bar Gidajensu bisa rikicin Boko Haram a jihar Borno.

Mutane sama da dubu 140,000 ne suka bar Gidajensu a shekarar 2019 kadai bisa rikicin Boko Haram a jihar, kamar yacce Majalissar Dinkin Duniya ta tabbatar.

A yayin wata ziyara da sakataren hukumar, Mark Lowcock, ya kai jihar Borno, ya bayyana cewa hare-haren Boko Haram ne suka tilastawa mutanen barin gidajensu a matsayin ‘yan gudun Hijira.

Sakataren ya kara da cewa zuwa yanzu; kusan mutane miliyan 3 ne suka fuskantar cikin tsananin rashin abinci a bisa rashin yin shuka da manoma basa iya yi a dalilin hare-haren ‘yan kungiyar Boko Haram.

A bangaren masu neman agaji kuwa, sakataren yace mutane miliyan 7 ne suka bukatar agaji a jihohin Adamawa da Yobe.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.