Duk wanda yace komai yana tafiya dai-dai a Najeriya, ‘Makaryaci ne Munafiki’ – Sheikh Gumi

Sheikh Dr Ahmad Abubakar Gumi ya ce ” MAKARYACI NE WANDA YACE KOMAI NA TAFIYA DAIDAI A NAJERIYA .”

Dr. Gumi ya bayyana haka ne a wajen tafsirin Al-Kur’ani da yake gabatarwa a cikin watan Ramadan a jihar Kaduna.

DaboFM ta tattaro cewa; Sheikh Gumi yana tafsirin Surah Taubah, aya ta 24.”

Gumi ya fara kokawa ne kan wata yarinya mai shekaru 6 da ta rasu bisa cutar Amai da Zawo, sai dai a cewarshi Likitoci sun gaza bata kulawa wajen riketa a asibitin domin cikakkiyar kulawa.

“Babu wani abu dake tafiya dai dai a kasar nan, babu shi, kuma duk wanda yace haka, makaryaci ne, munafiki.”

Komai yana tafiya a bai bai, kowa na kuka, sako baya zuwa kunnen shugaban kasa, a zatonshi komai yana tafiya dai dai.”

Majiyoyin DaboFM sun jiyo wasu ‘yan maganganun tsakanin masu sauraron karatun, inda wasu suke cewa “Mallam yana(Shugaban Kasa) ji.”

%d bloggers like this: