Najeriya kasa ce dake da tarin al’umma wadanda mafi yawansu matasa ne ‘yan kasa da shekaru 35.
Najeriya dai tana daga cikin jerin kasashe masu yawa a duniya.
Sai dai anan, mun zakulo wani garin da mutan dake rayuwa a cikinshi sunfi duk ‘Yan Najeriya yawa?
Nasan an cika da mamaki ko?
Wannan gari ba a ko ina yake ba illa kasar Indiya, kasar dake a matsayi na biyu a jerin kasashe masu yawa a duniya.
Tin a shekarar 2011, jihar Uttar Pradesh ta kere Najeriya a yawan mutane.
Adadin ‘yan jihar Uttar Pradesh(2011): 199,812,341
Adadin ‘Yan Najeriya(2019): 199,789,000*
Ga alkaluman adadin haihuwar da akeyi a Indiya da Najeriya.
A Indiya:
Ana haihuwar jarirai 2,062 a duk awa guda, inda ake samun 49,481 a kowacce rana, a kowanne wata, adadin yana kaiwa kusa miliyan daya da dubu dari biyar.
A Najeriya:
Ana samun haiwuwa miliyan 7 a kowacce shekara.
Bambancin:
Indiya tana samun jarirai miliyan 18 a kowacce shekara, ita kuma Najeriya na samun miliyan 7 ne kacal.
Tsiran da yakai miliyan 11 kowacce shekara.
Jihar Uttar Pradesh itace jiha mafi yawan al’umma a Indiya dama fadin Duniya baki daya.
In da jihar Uttar Pradesh kasa ce mai zaman kanta, itace zata zama kasa ta biyar a duniya a yawan al’umma.
Jihar na arewacin kasar Indiya, tana dauke da abubuwan tarihi dayawa.
Ginin Taj Mahal da yayi shura a duniya, yana gine ne a jihar ta Uttar Pradesh.