Gobara a KANNYWOOD: Ali Nuhu ya kai karar Adamu A. Zango Kotu bisa tuhumarshi da batancin suna

Karatun minti 1

Shahararre kuma fitattacen jarumi a masana’antar Kannywood, Ali Nuhu ya kai karar abokin sana’arshi Adamu Zango.

A wata majiyar sirri da muka bankado, mun samu labarin matakin da Ali Nuhu ya dauka na mika Adamu Kotu.

Ali Nuhu yayi koke kan cewa kotu tayi musu tsakani, tare da zargin Adamu Zango dayi masa sharri, kazafi da kuma kokarin yiwa rayuwarshi barazana.

Kotu ta umarci Adamu Zango daya bayyana a gabanta ranar Litinin, 15 ga watan Afirilun 2019.

Takardar Kotu

Kotu mai suna USC Fagge, ta umarci Zango ya halartar da gabanta da misalin karfe 8:30 na safe.

Ali Nuhu ya shigar da karar ne bisa neman kotu ta bisa bisa tsakani akan batancin suna da Zango yayi masa.

Kotu tace:

“Kotu tana kiran ka akan shari’ar da take gaban ta ta neman shiga tsakani akan bata suna don haka sai kazo kotu a wannan ranar dana ambata a sama.”

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Latest from Blog