Labarai

Zaben Indiya: Mutum miliyan 900 zasuyi zaben Firaminista a kasar Indiya

Yau 11 ga watan Afirilun 2019, al’ummar kasar Indiya suka fara jefa kuri’arsu.

Alkaluman da hukumar zaben kasar ta fitar ya nuna cewa mutane miliyan 900 ne zasuyi zabe a kasar.

Adadin masu kada kuri’ar ya karu da miliyan 70 inda a shekarar 2014, mutane miliyan 830 ne ke da rijista, miliyan 550 ne suka iya kada kuri’arsu a wancen lokacin.

Sai dai zaben kasar Indiya yasha bam-bam dana sauran kasashe, inda ake gudanar da zaben bai daya. Ana gudanar da zaben ne bisa jagawalin da hukumar zabe ta tsarawa kowacce jiha ranar da za’a gudanar da zabe.

Yaya yanayin ranakun zabe suke a kasar Indiya?

Hukumar zabe tana ware wadansu jihohi inda za’a fara zabe, kafin daga bisani ace anyi zabe a kowacce jiha. Kusan kowacce jiha tanada ranar zaben ta, amma akan iya samun wasu jihohin suyi zabe a rana daya.

Yaya ake zaben Shugaban kasa ko babban Minista?

A tsari na zaben Indiya, ba’a zaben shugaban kasa ko babban minista kai tsaye. Duk jami’iyyar data fi rinjaye wajen samun yawan ‘yan majalissun a matakin jiha da kasa, jami’iyyar ce zata kafa mulki a kasa ko Ministan jiha.

Jihar da jami’iyya tafi samun ‘yan majalissun jiha, ita zata fitar da babban minista, haka ma a wajen fitar da Fira Ministan Kasa.

Taya ake gudanar da zabe a Indiya?

Yanayin gudanar da zaben Indiya kusan iri daya ne da Najeriya, wajen tantance masu zabe da kuma yin zabe cikin akwatin daga kai sai kuri’ar ka tare da saka alama a yatsa domin gudun yin zabe sau biyu.

Sai dai ana amfani da na’ura wajen yin zaben, inda hotunan jami’iyyu suke fitowa a jikin na’ura, mai zabe zai danna alamar jami’iyyar da zai zaba.

Mai zabe zai iya kin zabar kowacce jami’iyya ta hanyar danna madannin “Babu jami’iyya datace in zaba.”

Daga cikin jihohin da ake gudanar da zaben yau, sun hada da yankin garin Kashmir, Jihar Arnunachal Pradesh, Sikkim, Nagaland, Uttarkhand, Meghalaya, Mizoram da kuma Telengana.

A makonnin shida masu zuwa kuma, za’a gudanar da zaben a jihohin Maharashtra, Uttar Pradesh (Jihar da tafi kowacce jiha a duniya yawan mutane), West Bengal da sauran wajaje.

Kasar Indiya dai kasa ce da take a matsayin na biyu bisa yawan al’umma, inda take da jiha guda daya datafi dukkanin mutanen Najeriya yawa, wato jihar Uttar Pradesh wacce take da mutane sama da miliyan 200.