Labarai

EFCC ta fara farautar ‘Yan Najeriya dake shiga NYSC da kwalin bogi musamman dan Kwatano

Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa ‘EFCC’ ta ce zata hada gwiwa da hukumar NYSC wajen farautar daliban dake aikin bautar kasa wadanda basu chanchanci shiga bautar kasar ba bisa rashin ingantacciyar takardar kammala karatu.

EFCC ta ce ta hukumar NYSC ce ta bukace ta da ta shigo domin fitar da A’i daga rogo, ma’ana tsame wasu ‘yan Najeriya marasa kishi wadanda suke siyarda kwalin karatunsu ga wadanda basu chanchanta ba domin yin bautar kasa.

DABO FM ta rawaito cewa shugaban riko na hukumar EFCC, Ibrahim Magu ne ya bayyana haka a birnin Abuja a dai dai lokacin da ya karbi bakunci Daraktan hukumar NYSC a ofishinsa dake Abuja.

A wata sanarwa a EFCC ta fitar a ranar Talata, ta rawaito Magu yana cewa hukumar EFCC zata bada gudunmawar ta wajen kame wadannan dalibai dake shiga bautar kasar da irin wadannan kwalayen karatun.

Yace, “Muna masu kushe al’amarin wasa marasa kishi, wadanda suke jawowa Najeriya abin kunya saboda kwadayinsu na samun kudi ko ta halin kaka, wanda ya hada da siyarda takardar kammala karatu ga daliban da basuyi karatu ba.”

Darakta NYSC ya roki EFCC da ta bawa hukumar goyon baya wajen yin duba tare da sa’ido ga su kansu makarantun da suke siyarda takardun kammala karatu ga wadanda basuyi karatun ba.

“Abin bai takaicin shine samun wasu manyan makarantu, musamman na garin Kwatano dake kasar Benin, suna turo mana mutanen da basuyi karatu bisa tsarin ba domin shiga shirin bautar kasa.”

“A yanzu haka, muna bincikar irin wadannan da ake kira “Wai sun kammala karatu”, wanda mafi yawa daga cikinsu basa iya rubuta kowacce kalmar turanci.

Karin Labarai

Masu Alaka

NYSC ta dakatar da sansanonin bautar kasa

Rilwanu A. Shehu

Katsina: Matasa 3 dake yiwa kasa hiduma a NYSC sun rasa Rayukansu a hatsarin Mota

Dabo Online
UA-131299779-2