Labarai

Dan Najeriya ya rasu jim kadan bayan kammala karatun Digiri na 2 a kasar Indiya

Dan Najeriya ya rasu jim kadan bayan kammala Digirinshi na 2 a kasar Indiya.

Dalibin, Sulaiman Abdullahi, ya kammala Digirinshi na 2 a fannin Fasahar Ilimin Na’ura mai kwakwalwa a jami’ar Nims University dake jihar Rajasthan a kasar Indiya.

Wakilin DABO FM a kasar Indiya, ya tabbatar da cewa Sulaiman, dan asalin jihar Adamawa, ya rasu a ranar Laraba bayan fama da matsananciyar rashin lafiya.

Ya kara tabbatar mana da cewa rashin lafiya tazo masa ne sakamakon sakon rasuwar mahaifiyarshi da ya riske shi kwana 2 bayan bikin kammala karatun da yayi.

Yanzu haka dai gawar Sulaiman ta na asibitin Sawai Man Singh (SMS Hospital) dake garin Jaipur a jihar Rajasthan, inda anan ne Allah ya karbi rayuwar Sulaiman Abdullahi.

Da zarar jami’an ‘yan sanda sun gama dukkanin binciken, majiya tace za’a binne mamacin a makabartar unguwar Amer dake garin Jaipur na jihar Rajasthan, arewacin kasar Indiya.

DABO FM ta binciko cewa marigayi Sulaiman, tsohon dalibin makarantar Elkanemi College of Islamic Theolology dake jihar Maiduguri (‘Yan rukunin 2013)

Ya kuma kammala karatun Digiri na 1 a jami’ar Nims University Indiya daga shekarar 2015 zuwa 2017 inda ya daura Digiri na biyu duk a jami’ar daga 2017 zuwa 2019 a fannin Fasahar Ilimin Kwafuta.

Karin Labarai

Masu Alaka

Mahaifin Umar M Shareef ya rasu

Dabo Online

BUK ta sake rasa Farfesa

Dabo Online

Jigawa: Dan Majalissar Tarayya ya sake rasuwa

Dabo Online

Umaru Musa ‘Yar Adua ya cika shekara 10 da rasuwa

Dabo Online

Sanata Imo ta Arewa ya mutu bayan faduwa a bayan gida

Dabo Online

Alƙalin alƙalan jihar Yobe, Musa Nabaruma ya rasu

Dabo Online
UA-131299779-2