Labarai

Akwai yiwuwar hana sana’ar tuka ‘Babur mai kafa 3’ a jihar Kano – Dan Agundi

Sabon shugaban hukumar KAROTA ta jihar Kano, Hon Baffa Babba Dan Agundi, ya bayyana cewa akwai yiwuwar hukumar ta haramta tuka babur din ‘Adaidaita Sahu’ a jihar.

Sashin Hausa na Jaridar ta rawaito cewa; Hon Baffa ya bayanna haka ne a ofishinsa yayin ganawarshi da manema labarai.

“Ko shakka babu, alamu na nuna yiwuwar dakatar da ci-gaba da aiwatar da sana’ar Adaidaita a fadin Jihar Kano baki daya, amma dai yanzu tukunna ba za mu ce komai ba a kan wannan sana’a da Matasan wannan Jiha ta yi wa rubdugu.” – Dan Agundi , Leadership Hausa

Ya bayyana cewa tini dai jami’an tsaro masu aiki a jihar suke bincike dan tattaro bayanai akai kuma da zarar sun kammala binciken itama hukumar zata yanke hukunci.

Ya kara da cewa hukumar ta KAROTA a shirye take da daukar kowanne mataki akan abinda take da hurumi don kare rayuka da tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Karin Labarai

Masu Alaka

Gwamnatin jihar Kano ta haramta lika hotuna ko rubutu a jikin motoci da babura masu kafa 3

Dabo Online
UA-131299779-2