EFCC ta kama wasu manyan ma’aikata 5 a Kano akan laifin cuta, yaudara da makirci

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ‘EFCC’ ta tuhumi wasu manyan ma’aikata 5 a jihar Kano cutar da sukayiwa wasu mutane akan sama musu aiki KAROTA.

EFFC ta tura wani Abduljalal Salisu da wadansu ma’aikata 4 na hukumar kula da titunan jiran Kano ‘KAROTA’ zuwa gaban mai Shari’a Faruk Lawal babbar Kotu jihar akan samun su da cuta da bada aiki bogi.

An chaji ma’aikatan bisa laifin cuta, damfara, da makirci wanda ya sabawa shashi na 96,97, 363 da 364 na kudin tsari.

Sai dai dukkanin wadanda ake tuhuma sun ki amsa laifin.

Lauyan masu kara (EFCC), Mr Micheal Ojo, ya bayyanawa kotun cewa; a watan Maris din daya gabata, ma’aikata sun shiryawa wani Anas Ahmad kitumurmura bayan sun alkauranta masa samun aiki a hukumar KAROTA.

Micheal Ojo ya kara da cewa, sun kuma bawa wani Sabiu Muhammad takardar kama aiki na dundundun wacce take ta karya.

Ya kuma duk dai a watan na Maris, wadanda ake tuhumar sun bawa wani Umar Habibu takardar karya ta daukan aiki a hukumar Ilimin Firamare ta jihar Kano.

Lauyan kare wadanda ake kara, Rabiu ABdullahi, ya roki kotu ta bada bailinsu bisa sashi na 35 na kudin tsarin mulkin Najeriya 1999.

Mai Shari’a Lawal Faruk ya bada bailinsu akan kudin Naira 250,000 ga kowannensu.

%d bloggers like this: