EFCC ta kame zababben dan Majalissar jihar Kwara akan cuwa-cuwar miliyan 26

Karatun minti 1

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta kama zababben dan majalissar jihar Kwara, Abdulgafar Ayinla, akan cuwa-cuwar Naira miliyan 26 na siyar da wani gida.

Dan majalissar ya karbi kudin ne akan cewa zai siyawa wata mata gida , mazauniyar kasar Amurka gida a garin Ilorin na jihar Kwara.

Ayinla, wanda ake saka ran rantsar dashi ranar 29 ga watan Mayu, 2019, ya shaidawa EFCC cewa lallai yaci kudaden, sai dai yace yayi amfani da su ne wajen yin yakin neman zaben shi.

Mai magana da yawun EFCC, Tony Orilade yace Ayinla yayi alkawarin biyan kudin ne idan ya karbi alawus din da za’a basu na sharar fage na shiga majalissar.

Wacce ta kai karar, ta kasance mazauniya ce a kasar Amurka, inda da bayyana cewa; ‘yar uwarta ce ta hada ta da Ayinla, akan zai taimaka mata wajen siyan gida a Ilorin.

EFCC ta bayyana cewa nan bada dadewa ba zata maka zababben dan Majalissar a Kotu.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog