Labarai

El-Rufa’i ya fara sintiri domin hana Kanawa shiga jihar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufa’i ya shiga sintirin hana yan jihar kano shiga jihar sa bikin Sallah.

Dabo FM ta hango gwamnan jihar Kaduna, El-Rufa’i a shafin sa na kafar sadarwa yana bayyana tini ya fito domin hana Kanawa shiga jihar domin bikin sallah, duba da yanda jihar Kano ke fama da masu dauke da cutar Kwabid19 da suka kara yawaita a jihar wanda ita ce ke matsayin ta 2 a wanda sukafi kamuwa da cutar a fadin Najeriya.

Sakon dai na fadin Gwamna El-Rufa’i ya fito a rana ta biyu domin hana zirga zirga jiha zuwa jiha.

Kwanaki kadan da suka wuce ne dai Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya chafke motoci masu yawan gaske tare da mutane da suka haura dari masu neman shigowa jihar Kano a wani yunkuri da gwamnan yayi na maida martani ga gwamnan Kaduna.

Karin Labarai

UA-131299779-2