Labarai

Yadda jaruman Kannywood suke taimaka wa yaduwar labaran bogi

A dai dai lokacin da ake kokari kawar da yada labarun bogi a kafafen sadarwa, wasu daga cikin fitattun jarumai a Kannywood suna taimakawa wajen kara yaduwar labaran.

DABO FM ta tattara yadda wasu daga cikin jarumawan suka rika yada wani faifan bidiyo da nufin ‘cewar kasar Saudiyya ta nemi afuwa bayan kuskeren sanar da ganin watan Shawwal.’

DABO FM ta binciko yadda jarumi Sani Musa Danja da jaruma Hafsat Idris suka yada bidiyon a shafukansu na sada zumunta.

Daga Shafin Instagram na Jarumi Sani Danja.

Binciken masana bin duddugin labarai musamman na bidiyoyi da sautin murya ya tabbatar da cewar bidiyon na bogi ne.

Kazalika DABO FM ta tabbatar da cewar babu rahoto sahihi da ya nuna haka.

Sai dai a shekarar 2015, an taba samun rahotanni daga wasu kafafen yada labaran mabiya Shi’a da suka rawaito cewar “Malamai Tunusia da Saudiyya sun bayar da hakurin kuskere wajen sanar da ganin wata”, shi ma dai babu wata ingantacciyar kafa da ta tabbatar da hakan.

Masu Alaka

Yacce yan matan Kannywood suka shilla yawan shakatawa a manyan biranen duniya

Faiza

Gobara a KANNYWOOD: Ali Nuhu ya kai karar Adamu A. Zango Kotu bisa tuhumarshi da batancin suna

Dangalan Muhammad Aliyu

Gobara a Kannywood: Mun sasanta da Mustapha Nabruska – Hadiza Gabon

Dabo Online

#SunusiOscar442: Adam A. Zango ya fice daga Masana’antar Kannywood

Dabo Online

Kotun ta bawa CP Wakili umarnin kama Hadiza Gabon

Dabo Online

Nabruska ya dakatar da fitowa a Fim din Hausa bisa nuna rashin goyon bayan kamun Sunusi Oscar

Dabo Online
UA-131299779-2