Lokaci ya yi da Adhama zai farfado da ofishin sa daga magagin mutuwa -SG SUG BUK

Karatun minti 1

Shugaban kungiyar daliban jami’ar Bayero, Mahmoud Balarabe Yazid ya yi kira ga mai bawa shugaban kasa shawara ta fannin matasa da dalibai, Nasir Sa’id Adhama da ya farfado da ofishin sa ya wayar da kan matsa domin samun gajiyar kudin da gwamnati ta ware wa asusun matasa.

Rahoton DABO FM ya bayyana shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya ware kimanin naira biliyan 75 domin tallafawa matasa su zauna da kafafun su wajen kirkire-kirkire na fasaha tare da rage talauci ga kasa baki daya.

Mahmoud ya bayyana tun dai bayan zuwan mai bawa shugaban kasa shawara a shekarar 2015 ofishin ya shiga wani hali wanda ya koma tamkar babu ofishin a Najeriya.

Yace “Lokaci ya yi da Nasir Adhama zai amfani da wannan dama domin farfado da ofishinsa tun bayan da ofishin ya dena aiki a shekarar 2015 da aka nada shi mukamin mai bawa shugaban kasa shawara a fannin matasa da dalibai.”

Wannan kalamai sun biyo bayan kallon da mutane suke wa ofishin na Adhama na rashin aikata katabus tun bayan samun wannan mukami da yayi a shekarar 2015.

Mahmoud ya kara da cewa “Kayi amfani da wannan dama (N75b Nigeria Youth Investment Fund) domin wayar da kan matasa yanda zasu ci gajiyar gwaggwaban tallafin domin gudun kada a maimaita abinda akayi a shirin YouWin.”

Da dama mutane sun mance da ofishin yana aiki kaman yanda suka bayyana a lokacin da suke bayyana ra’ayin su.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog