Farashin Buredi zai iya yin tashin gwauron zabi – Kungiyar AMBCN

Farashin Buredi dama kayan ci na dangogin fulawa Najeriya zasu yi tashin gwauron zabi kamar yadda kungiyar masu gasa Buredi ta Najeriya suka bayyana.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, kungiyar tace yiwuwar karin farashin na zuwa ne bayan karin kudin buhun fulawa akasamu na Naira 600.

A watan daya wuce na Maris, farashin fulawar yana kamawa N10,200 da N11,300 wanda a yanzu bayan karin Naira 600, farashin yake kamawa N10,700 da N11,900.

Da yake bayani jiya a jihar Borno, shugaban kungiyar, Dominic Daniel Tumba Turi, yace masu dillancin fulawar “sun kara kudinne ba tare da tuntubarsu ba duk da kasancewar wanda ke siye fulawar da kaso 80 cikin 100.”

Daga karshe yayi kira da gwamnati data shigo cikin lamarin domin samun daidaito.

“Mun san idan muka kara farashin, mutane zasu fito zanga zanga, to lallai yakamata gwamnati ta shiga lamarin domin tasa su janye karin amma in bahaka ba zamu kara farashin muma.”

A waya da Jaridar DAILY TRUST tayi da shugaban kungiyar na jihar Borno, sunce kudin zai karu ne da kaso goma.

%d bloggers like this: