Mulkin APC: Zaben2019 ‘Inconclusive’, Jamb 2019 ‘Inconclusive’, Daga Dangalan Muhammad Aliyu

Kasancewar shekarar 2019 ta fara nisa, sabbabin al’amura na ban mamaki sun faru kama daga sabgogin zabe dama wasu batutuwa da gwamnatin APC take rajin fada wanda kowa yasan karairayi ne masu lasisi daga gwamnatin tarayya.

Zaben2019, zabe ne mai ban mamaki wanda yasha bambam da zaben 2015, zaben da duniya ta shaida cewa an gudanar dashi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali tare da barin dimokradiyya tayi aikinta wajen baiwa talakawa abinda suka zaba.

2019 shekara ce da duk dan dimokradiyya bazai manta da ita ba, musamman yan jihar Kano da akayi mana fashi da makamin abinda muka zaba zaben Gwamna.

Gwamnatin APC tayi amfani da kalmar “INCONCLUSIVE” wajen yiwa dimokradiyya karan tsaye.

Dokar hukumar zabe tace duk dan takarar da yake da kuru’u mafi rinjaye tare da samun nasara a 1 bisa ukun kananan hukumomin jiha, za’a sanar dashi a matsayin sabon Gwamnan wannan jihar. Amma gwamnatin sama tayi amfani da kalmar ‘Inconlusive’ a jihohin da PDP take jan ragama da kuma jihar Taraba domin yin basaja.

Kwatsam bayan kammala zana jarrabawar JAMB ta shekarar 2019, hukumar jarrabawar take ta wasa da hankalin Dalibai dama iyayensu wajen kin bayyana musu sakamakonsu.

Hukumar ta bada 29 ga watan Afirilu domin fito da sakamakon jarrabawar, sai dai har yau 30 ga wata, munji shiru kamar an aiki shirwa.

Yanzu dai ta tabbatar Jamb tace wai an samu yin satar amsa dayawa a dakunan jarrabawar, an kama wasu dalibai da sukaje rubuta jarrabawar tare da katinan shaidar wasu daliban daban.

Hakan yasa hukumar tace akwai yiwuwar sake jarrabawar baki daya.

%d bloggers like this: