Sheikh Pantami yayi kira da acigaba da goyawa Buhari baya don cigaban Najeriya

Shashin Hausa na Jaridar Leadership ya rawaito Sheikh Pantami yana tsokaci tare da kiran Malamai su marawa shuwaganni baya a wani taro daya halarta na bitar maluman Izala da zasu gabatar da Tafsiri a watan Ramadan.

” Sheikh (Dr.) Isah Ali Ibrahim Pantami ne ya yi wannan kira a lokacin da ya ke jawabi ga cincirindon malamai da su ka taru a bikin rufe taron kara wa juna sani na kwanaki uku, wanda sashen ilimintarwa na kungiyar Izalatil Bida’ah Wa Ikmatis Sunnah [JIBWIS] mai hedkwata a Jos ta gudanar a dakin taro na makarantar kimiya na kungiyar da ke a titin Zariya da ke Jos ranar Lahadin da ta gabata.

Ya ce, yawan abubuwan assha da ke faruwa a wasar nan a yanzu irinsu ba ya faruwa shekaru 30 da su ka gabata. Ya furta cewa, shan muggan kwayoyi, kamar su kodin da wadansu ababen sa maye, yawan zinace-zinace da yin luwadi da madigo da aikin ta’addanci, kamar garkuwa da mutane a nemi fansa, da yawan sace-sacen shanu da kashe masu shanun da sace matayensu a yi mu su fyade, abu ne da ya ke ci wa wannan gwamnati tuwo a kwarya.

Dr. Pantami, wanda shi ne darakta janar na hukumar kimiyya ta tarayya ta NITDA kuma babban bako mai jawabi a gurin bikin bitar, ya ce, “ba abinda ya fi damun shugaban kasa Muhammadu Buhari kamar matsalar rashin tsaro a kasar nan, musamman a jihohin Arewacin kasar.” Don haka sai ya kara yin kira ga malaman da su kara jajircewa wajen yin wa’azuzzuka a kan abubuwan da Allah (SWT) ya yi haramci a kan aikata su da irin sakamakon masu aikata su za su samu idan su ka mutu ba sa tuba ba.

Ya yaba bisa nasarorin da gwamanati mai ci yanzu karkashin jagoranci shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu wajen yin yaki da ’yan Boko Haram, wanda ya ce, a gwamnatin da ta gabata karkashin shugabanci Goodluck Jonathan, wanda ya nuna juyayinsa bisa dimbin malaman addinin Musulunci da ka yi rashin su da kuma dubun-dubatar mutanen da a ka yi rashin su a tashin bama-bamai da a ka yi tayi a manyan garuruwan kasar nan, sai ya bukaci al’ummar kasar da su kara bai wa Buhari goyon baya, don ya sami kwarin gwiwar maida kasar kan tafarki mai kyau wanda mutumin kasar nan zai yi alfahari da ita a duk inda ya ke a duniya.

A jawabinsa mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai na tarayya, Hon. Idris Ahmad Jaje, wanda Dr. Yahuza Jama’are ya wakilta, ya yaba bisa kokarin da kungiyar ta ke yi wajen ilimintar da al’ummar kasar kuma ya bukaci al’umma da su cigaba da yin addu’o’in samun zaman lafiya mai dorewa da cigaban tattalin arzikinta.

A jawabinsa shugaban majalisar malamai na JIBWIS na kasa, Shiekh Muhammadu Sani Yahaya Jingir, ya hori malamai 530, wadanda kungiyar za ta tura tafsiri a azumin wannan shekara a wurare daban-daban ciki har da wajen Najeriya da su yada darussan da su ka koya a wajen bitar, kuma su zama jakadu nagari a duk inda a ka tura su yin tafsirin.

Da ya ke jawabin bayan taron bitar ko’odinatan shirya bitar Al-Hafiz Aminu Yusuf Nuhu ya ce, taron karawa juna ilmin ya sami mahalarta masu bita 1,121 daga jihohi 31 na kasar nan da kuma kasar Nijer, inda Filato da Bauchi ke kan gaba da mahalarta 194 da 218 kowanne.”

Leadership HAusa.

%d bloggers like this: