Farashin gangar danyen man fetur ya tashi da kashi 6 a kasuwar duniya

Karatun minti 1

Gangar danyen man fetur yayi tashin gwauron zabi a kasuwar duniya da kashi 6 a satin daya gabata.

Hakan na zuwa ne yayin fargabar hari da sojojjin kasar Amurka suke shirin kaiwa kasar Iran wanda hakan zai kawo karancin man fetur a kasuwar duniya.

DABO FM ta rawaito daga Jaridar Business Times cewa kasar Iran ce take samar da fiye da kashi 5 na danyen mai dake kasuwar duniya.

Farashin kamfanin Brent ya kai dalar Amurka 65.47 (N‭20,007. CBN) duk gangar mai daya.

Farashin ragowar kamfanunuwa ya tashi da kashii 4.3 a ranar Alhamis inda kasuwar ta tashi dai dai lokacin daya kai zuwa kshi 6 a karon farko cikin sati 5.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog