Labarai

‘Yan gudun hijira a Zamfara sun fara komawa gidajensu bayan samun ingantuwar tsaro

Sakamakon samun zaman lafiya da jami’an tsaro suka samo, yasa ‘yan gudun hijira da dama sun fara kaura daga sansaninsu zuwa garuruwansu na asali a jihar Zamfara.

Yusuf Idris, babban mataimakin gwamnan jihar kan harkokin yada labarai ne ya sanar da haka a wata takardar mai dauke da sa hannunshi daya baiwa manema labarai a ranar Juma’a.

‘Yan garuruwan Liko, Fura Girke, Kowha, Kundumau, Yargeba da Bundugel sun fara koma garuruwansu tin ranar Alhamis.”

Alhaji Abubakar Muhammad Dauran, mataimakin gwamnan jihar kan sha’anin tsaro ne ya jagoranci maida ‘yan gudun hijirar zuwa garuruwansu.

“ Da dama daga cikin ‘yan gudun hijiran sun yi zama a sansanonin dake garin Mada, karamar hukumar Gusau na tsawon watanni shida. Sannan wannan gwamnatin Matawalle ta tabbatar musu da tsaron rayukan su da dukiyoyin su.

Gwamnan jihar Bello Matawalle ya mika godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a dalilin karo jami’an tsaro da aka yi da kuma ci gaba da fatattakar mahara da dakarun Najeriya ke yi.

Matawalle ya kuma yi kira ga mutane kan ci gaba da yi wa jihar addu’a sannan ya yi kira ga manoma su fara shirin komawa gona domin zamn lafiya na dindindin ya fara dawowa jihar.

Karin Labarai

Masu Alaka

Sarkin Zurmi na Zamfara ne yace a kashe dukkan mutanen Dumburum – Gov Abdul’aziz Yari

Dangalan Muhammad Aliyu

‘Yan Bindiga da dama a Zamfara sun zubar da makamansu tare da neman yafiya – Matawalle

Dabo Online

Mutum 42 sun rasa rayukansu a harin da ‘Yan Bindiga suka kai wasu kauyukan jihar Zamfara

Dangalan Muhammad Aliyu

An saukar min da wahayi zanyi shugabancin Najeriya -Yariman Bakura

Muhammad Isma’il Makama

Rikicin Zamfara: Rashin adalci ne ace ban damu da kashe kashen Zamfara ba – Buhari

Dabo Online

‘Yan Bindiga a Zamfara sun kashe shugaban ‘Yan Banga

UA-131299779-2