(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Ke kaza kinzo da tone-tone, kin tona rami har hudu dan garaje – Sarkin Waka

Karatun minti 1

Shararren mawakin wakar Hausa, Naziru M Ahmad, yayi martani da wasu kalamai da suke nuni da yayi su ga gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Wannan ne karon farko da Naziru, Sarkin wakar San Kano, ya magantu tin bayan da gwamnatin jihar Kano ta kara yawan masarautu 4 a jihar Kano.

A irin salon su na mawaka, DABO FM ta rawaito Sarkin Waka yana kalaman habaici ga gwamnan jihar Kano tare da yabo da nuna goyon bayan ga Sarkin Kano Muhammdu Sunusi II.

Wakar mai suna “Mata ai kidan Tabare”

“Shekara dubu ana tare. Ke kaza kinzo da tone-tone, kin tona rami har hudu dan garaje.”

“Sarki mai martaba, iko na Allah wannan tabbata ne, mai ja da yin Allah dan wahala ne, mai shawara aiki nai bashi baci, makaryaci kullin dan yaudara ne, mu bauta Allah shine wanga zance, mai bin iyaye wannan ya riki dace”

“In sun so Sunusi sarkin su, inma basa so Sunusi sarki su.”

Za’a iya ganin tallar da DABO FM ba tada hurumi akai.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog