Labarai

‘Fasa Kwauri’ ya karu duk da rufe iyakokin Najeriya

A kasuwar Limbe dake kudu maso yammacin Kamaru, masu saye da sayarwa na cikin gida da na Najeriya sun ce tun bayan da gwamnatin Najeriya ta rufe bakin iyakokin ta, kasuwancin su ya fuskanci koma baya.

Yan kasuwar sun ce suna yawan samun karancin kayayyaki daga kasashen biyu, abinda ya janyo hauhawar farashen kayayyaki da kashe 15 cikin 100.

Wata matashiya ‘yar shekara 35 da haihuwa mai suna Miracle Ademola, na saida riguna a Kamaru daga nan kuma sai ta sayo shinkafa don ta saida a Najeriya. Ademola ta koka akan makudan kudaden shiga da fitar da kayayyaki ta jirgin ruwa da ake sanyawa.
Hukumar kididdigar Kamaru ta ce kusan ‘yan kasar ta 15,000 ne ke kasuwanci a tsallaken iyakar Najeriya.

Hakazalika su ma ‘yan Najeriya suna zuwa Kamaru sarin kayan gona, ciki har da shinkafa, albasa, auduga da ma shanu don ‘yan kasuwar su.
‘Yan sanda da jami’an kwastam a kudu maso yammacin garin Buea dake Kamaru sun kona wasu magunguna masu yawan gaske da aka yi fasa kwabrin su daga Najeriya ranar Lahadin da ta gabata.

Masu sukar lamiri sun ce rufe iyakokin Najeriya ya kawo shakku akan yarjejeniyar cinikayya ba tare da wani shinge a nahiyar Afrika da aka cimma a watan Yulin shekarar 2018.

Amma hukumomi a Najeriya na jaddada cewa har yanzu kofofin kasuwancin kasar na nan bude ta tashoshin jiragen ruwa.

Source: VOA HAUSA

Masu Alaka

Ginin babban dakin karatun Abuja zai lakume Naira biliyan 50 – Ministan Ilimi

Dabo Online

An saukar min da wahayi zanyi shugabancin Najeriya -Yariman Bakura

Muhammad Isma’il Makama

Najeriya Muna Da Gajen Hakuri Wallahi,shin ko za mu tuna

Rilwanu A. Shehu

A najeriya, an haifi Jarirai sama da 26,000 a daren sabuwar shekarar – UNICEF

Dabo Online

Nima na cancanci samun kyautar wanzar da zaman lafiya ta ‘Nobel Prize’ -Buhari

Muhammad Isma’il Makama

Yanzun nan: Soja ya kashe abokin aikinshi da farar hula mace daya a jihar Osun

Dabo Online
UA-131299779-2