//
Wednesday, April 1

CoronaVirus: Saudiyya ta bude Masallatan Makkah da Madina

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Kasar Saudiyya ta bude masallacin Harami na garin Makkah da na Ma’aiki SAW.

Hukumomin kasar sun dai rufe wuraren da suke mafi daraja biyo bayan fargabar yaduwar cutar Corona Virus tsakanin masu aikin Umara da zuwan bude idanu.

Gidan Talabijin na Al Ekhbariya ne ya rawaici hakan a ranar Juma’a bayan da ya rawaito cewar an kammala yin rigakafin daukar cutar da yadata a cikin wuraren da suke mafi daraja a idanuwan musulman duniya.

Saudiyya dai ta dakatar da bakin da suka zo kasar daga sashin duniya daga kasashe 25 domin hana yaduwar cutar.

Haka zalika, hukumomin kasar sunce dan yankin Larabawa da yaje sauran sassan duniya bazasu shiga kasar ba sai sun shafe kwanaki 14 cikin koshin lafiya.

Masu Alaƙa  'Yar Saudiyar da tayi ridda, ta samu mafaka a Canada

Zuwa yanzu dai an samu masu cutar Corona Virus guda 5 a kasar.

Ba’a samu tabbacin barin masu aikin Umara zuwa ziyartar wurare masu darajar ba.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020