Home Labarai#FreeDadiyata: Dadiyata baya hannun jami’an DSS

#FreeDadiyata: Dadiyata baya hannun jami’an DSS

by Dabo Online
0 comments

Jami’an tsaron na DSS sun bayyana cewa dan gwagwarmayar nan na darikar Kwankwasiyya baya hannunta.

Hukumar ta nesanta kanta daga tsare Idris wanda akafi sani da Dadiyata biyo bayan da mai magana da yawun dan takarar gwamnan jihar Kano, Sunusi Bature Dawaki, ya fidda bayanin zargin DSS da kama Dadiyata.

Sai dai a nata bangaren, hukumar ta DSS reshen jihar Kaduna ta hannun mai kakakinta, Peter Afunnaya da Daraktan ta Ahmad Koya, sun nesanta kansu da kama Dadiyata.

“Babu Abubakar Idris Dadiyata a cikin jerin sunayen wadanda muke tsare dasu. Bamu kamashi ba, kuma babu wani abu makamancin hakan daya faru a wannan daren.”

Hukumar ta bayyana haka ne a lokacin da suke magana ta wayar tarho da wakilan Jaridar Daily Nigerian.

Suma a nasun bangaren, rundunar ‘yan sandan jihar ta hannun kakakinta, Yakubu Sabo, yace suna cigaba da bincike don gano takamai-mai gurin da yake.

Tin dai a daren ranar Juma’a ne dai rahotanni suka tabbatar da kama Abu Hanifa Dadiyata, fitaccen mai fafukuta a shafin Twitter.

Dadiyata yayi suna wajen sukar lamiran gwamnatocin da ke mulki na APC a Najeriya, musamman a jihar Kano.

Duba da kasancewarshi mai kare muradin tafiyar tsohon gwamnan Kano, Dr Kwankwaso, Dadiyata yayi suna wajen caccaka da sukar gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00