Labarai

Babu bambanci tsakin Abubakar Shekau da Ibrahim Zakzaky – Muhammad yayan Zakzaky

Sheikh Muhammad Yakubu Al-Zakzaky, dan uwan shugaban kungiyar IMN ya bayyana cewa babu wani bambanci tsakanin ‘dan uwan nashi da Abubakar Shekau.

DABO FM ta binciko cewa; Sheikh Muhammad Al-Zakzaky ya bayyana haka ne a yayin wata ganawarshi da jaridar The Nation.

Da yake bayani kan haramta kungiyar IMN ta Shi’a da gwamnatin Najeriya tayi, babban yayan Sheikh Ibrahim Zakzaky yace “Tin da wuri yakamata gwamnatin ta haramta kungiyar.”

Sheikh Muhammad Al-Zakzaky dai shine shugaban kungiyar Izalatul Bidi’a Wa Ikamatussunnah reshen garin Zaria.

Ya kumayi kira ga gwamnatin tarayya da ta haramta bangaren Shi’a baki daya ba iya kungiyar IMN ba kadai.

Ya bayyana cewa akwai dangantaka tsakanin kungiyar IMN, Shi’a da Boko Haram inda ya kara da cewa “da Abubakar Shekau da Ibrahim Al-Zakzaky duk ‘yan ta’adda ne.”

Sheikh Muhammad Al-Zakzaky ya bayyana cewa shugaban kungiyar IMN, Sheikh Ibrahim Zakzaky shi da kanshi ya janyowa kanshi domin yasha yi masa kashedi akan abinda yakeyi na hatsari amma baya ji.

Yace: “Kamar yacce kuka sani, ni yayan Ibrahim Zakzaky ne, mahaifinmu daya, ya shiga Shi’anci a lokacin da muka fara tasowa. Bani da wani aboki kamarshi, tare mukeyin komai. Tare mukayi karatun Addinin Musulunci.

“Munyi masa kashedi akan Shi’ancin da yakeyi. Ni da kaina nayi masa kashedi sau dayawa amma yaki ji, bani da zabi sai dai in kyaleshi. Dan haka duk abinda hukumomi sukayi masa, shi ya siya da kudinshi.”

“Babu wani abu mai kyau a tattare da Shi’anci. Tin da dadewa yakamata gwamnati ta haramta ayyukansu, amma ta jira sai yanzu da suka wuce gona da iri.

“A duk duniya, ina aka taba ji cewa an tare wa shugaban Hafsin Sojojin kasa hanya suka hanashi wucewa? Tin a lokacin yakamata a tsayar da su. Amma sai yanzu gwamnati ta gane nufinsu.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Gwamnatin tarayya ta kammala shirin bayyana kungiyar Al-Zakzaky a matsayin ‘Kungiyar Ta’addanci’

Dabo Online

Akwai alamun Sheikh Zakzaky zai koma Najeriya cikin kwanaki 3

Dabo Online

Rahotan Dabo FM na yiwuwar dawowar Zakzaky Najeriya cikin kwanaki 3 ya tabbata

Dabo Online

Hotuna: Sheikh Al-Zakzaky ya tafi kasar Indiya neman magani

Dabo Online

Shugaban ‘Haramtacciyar’ kungiyar IMN ta Shi’a, Mal. Ibrahimul Zakzaky ya tashi zuwa kasar Indiya

Dabo Online

Gwamnatin Kaduna zata daukaka kara akan izinin Al-Zakzaky na zuwa Indiya

Dabo Online
UA-131299779-2